Gwamnatin Jigawa ta rufe dukkan makarantu saboda barazanar tsaro

0
76

Gwamnatin Jigawa ta ce ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantu a fadin jihar saboda barazanar tsaro. A cewar NAN, kwamishinan ilimi na jihar Lawan Yusuf ya tabbatarwa manema labarai hakan a ranar Laraba a Dutse babban birnin jihar Jigawa.

Jaridar TheCable ta ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga suka kashe jami’in hukumar shige da fice ta kasa (NIS) tare da raunata wasu mutane biyu a makon jiya a jihar.

Yusuf ya ce gwamnati ta samu rahoton sirri kan yiwuwar kai hare-hare a dukkan makarantun kasar.A cewarsa, rahoton ya mayar da hankali kan makarantun da ke jihohin kan iyaka, inda ya kara da cewa an rufe dukkan wuraren koyo a Jigawa.

Ya ce an sako daliban da suka hada da wadanda ke koyo a makarantun kwana daban-daban na jihar domin komawa gida.Makarantun Sakandare da ke fadin jihar an ce sun sanya ranar Juma’a a matsayin ranar da daliban zasu kammala jarrabawar zango na uku.

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) an ce an tattara su zuwa makarantun jihar yayin da daliban da har yanzu ba su kammala jarrabawar zango na uku ba aka umarci su koma gida.Jigawa na daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya dake kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar.

Jihar ta sha fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron mazauna yankin tsawon shekaru.

UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.