“Ba ni da niyyar mayar da Legas babban birnin Nijeriya'”- Tinubu

0
20

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba shi da niyyar mayar da Legas babban birnin Nijeriya daga Abuja.

Mai bai wa shugaban kasar shawara kan watsa labarai da tsare-tsare Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafin X.

“An soma watsa irin wadannan jita-jitar a lokacin yaƙin neman zabe a bara, inda ƴan adawa ke neman duk wasu hanyoyi na daƙile yakin zabe na,”a cewar sa

Ya bayyana cewa masu watsa irin waɗannan labaran ba su da gaskiya sannan ya kara bayyana na su a na gaba-gaba wajen nuna kabilanci a fadin kasar.

“Batun mayar da FAAN Jihar ta Legas, wanda sashe ne a ƙarƙshin Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama, kuma tun asali a can yake da zama kafin tsohon minista Hadi Sirika ya mayar da shi birnin Tarayya a gwamnatin baya, kuma duk ba shi ke nufin za a mayar da babban birnin Nageriya ta Legas ba.”

Haka kuma ya bayyana cewa bai kamata a razana da batun mayar da wani sashe na Babban Bankin Najeriya zuwa Legas, sakamakon akasarin bankunan kasar hedikwatarsu tana can Legas din.

Daga karshe ya bayar da misali kan cewa akwai ma’aikatun gwamnatin Nijeriya da hedikwatarsu ba a Abuja take ba, wadanda suka hada da NIMASA da NPA ke Legas haka kuma akwai NIWA da ke Lokoja.

 

 

 

Hafsat Ibrahim