Fashewar wani bolan karfe a Maitama ba shi da alaka da bam;In ji Rundunan Yan Sandan Najeriya.

0
18

Yan sanda a babban birnin tarayya ta karyata ikirarin da ake yi na cewa an kai harin bam a ofishin BPE da ke  gundumar Maitama, yayin da ta ci gaba da cewa lamarin fashewar wani abu ne daga wani kwandon karfe na zuba shara.

Lamarin da ya faru ne a wata rumfar shara a wajen harabar ofishin hukumar da ke Maitama,  da yammacin yau Laraba.

Sai dai, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, yayin da take sabunta wa jama’a bayanai, ta bayyana cewa binciken farko da sashen da ke kula da harba ababen fashewa ya nuna cewa wata kwantena ce na Kare da ta yi zafi ta kunna wuta yayin da wani abu ya fashe.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Josephine Adeh, ta fitar ta ce, “An tura wata tawagar gaggawa tare da jami’an sashin kawar da bama-bamai domin tantance halin da ake ciki, kuma binciken farko ya nuna cewa wani kwandon shara da ya wuce kima na karfe da aka kunna wuta a ciki ya dau zafi mai tsanani, ya fashe,  wanda ya yi sanadiyar raunata mutane biyu daga cikin masu kwashe shara, wadanda a halin yanzu ke samun kulawar likitoci a babban asibitin Maitama.

“Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da kaurace wa amfani da kwandon shara na karfe. Maimakon haka, muna ba da shawarar yin amfani da kwantena filastik ko roba don zubar da sharar gida, saboda suna haifar da haɗari ga rayuwar al’umma.

 

Daga Fatima Abubakar.