BABBAN KOTUN TARAYYA DA KE ABUJA TA AMINCE DA CI GABA DA TSARE KYARI DA WASU MUTANE SHIDA HAR TSAWON KWANAKI 14.

0
191

A ranar talata da ta gabata ne,wani babban kotu da ke Abuja,ta ba hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa,izinin ci gaba da tsare mataimakin kwamishinan yan sanda Abba kyari da aka dakatar da wasu mutum shida.

Mai shari’a Zainab Abubakar,ta bayar da umurnin ne,da a ci gaba da garkame mutane 7 da ake tuhuma har sai an kammala bincike.

Sauran mutanen sun hada da :

1-Mataimakin kwamishinan yan sanda Sunday Ubia,

2-Mataimakin sufeto Bawa James.

3-sufeto Simon Agirigba.

4-John Nuhu.

5-Emeka Alphonsus.

6-patrick Chibunna.

Mai shari’a Zainab ta bada umurnin ne bayan da ta saurari daraktan masu gabatar da kara na NDLEA Joseph Sunday wanda ya tura takardan neman aiki gaban kotun.

Hukumar ta NDLEA a cikin takardan,ta nemi karin lokaci na ci gaba da tsare kyari da sauran mutanen a dalilin fataucin miyagun kwayoyi da ake zargin su da shi.

By Fatima Abubakar