GOBARA TA LASHE WANI SASHE NA HEDIKWATAR MA’AIKATAR KUDI TA TARAYYA ABUJA.

0
84

Da misalin karfe shida da minti hamsin ne na safiyar yau laraba,gobara ta tashi a wani sashe na Hedikwatar ma’aikatan kudi na tarayya Abuja.

Wutan ya tashi ne a wani gini na kasa ,wurin da ake aje batura na na’urar inverter ,a sanadiyar fashewar daya daga cikin baruran.Kuma kimanin batura 16 ne abin ya shafa.

Wani ma’aikaci a Hedikwatar, yace tarwastewan wuta a dakin na inverter shine makasudin wutan,amma lamarin bai yi barna sosai ba.

Da yake zantawa da manema labarai a harabar ta Hedikwatar, kakakin ma’aikatar Mr Olajide Oshundun,yace sun fara ganin hayaki ne idan ya jawo hankalin jama’a, nan take aka gaggauta kawo dauki wurin kashe wutan kafin Hukumar kashe Gobara na tarayya ta iso.

Olajide ya kara da cewa,cikin minti 15 zuwa 20 ne aka kashe wutan.

By Fatima Abubakar.