Bayan Barazanar Raba Jiha: An Yi Zaman Sulhu Tsakanin Atiku Da Kauran Bauchi

0
5
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, a ranar Talata ya zauna da dan takarar kujerar shugaban kasan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a Abuja. Wannan ganawar ta auku ne biyo bayan rahotannin cewa gwamnan na Bauchi ya yi barazanar hannun riga da yakin neman zaben Atiku a 2023.
A jawabin da ya fitar, Gwamnan yace: “Yau, na jagoranci masu ruwa da tsakin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) na jihar Bauchi zuwa wajen dan takaran kujerar shugaban kasa PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a Abuja.
Abubuwan da muka tattauna a kai sun hada da cigaban jam’iyyarmu.” Gwamna Bala ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

Daga Faiza A.gabdo