Yadda zamu cire zanen jiki (stretch marks)

0
75

Wannan saukakeken hanya da zamu bi wajen magance layin jiki da man gida. Hanyoyin da zamubi shine sinadarai masu muhimmanci guda uku wadanda su ne:
1) Man shanu
2) Ruwan Beets
3) Aloe Vera Gel

Yanda zamu hada
Don shirya wannan kirim mai sauƙi na gida don cire alamomi, za ku buƙaci samun babban kwano yanda zaku samu damar haɗawa da kuma kayan aiki daidai yanda kuke da bukata.
• Azuba babban dunkule na man shanu a cikin kwano a zuba cokali 1 na ruwan Beets. Sannan a dama a hankali kuma akai-akai har sai ruwan beets din ya haɗu da man shanun.
• Asa Aloe Vera Gel a ciki sai a kara hade su da kyau, idan sun hadu sai a rinka shafawa kadan kadan akan fata don ganin ko hadin ya zama kirim sosai.  Idan hadin yayi shikenan sai a rinka shafawa a wajen.

Daga Faiza A.gabdo