![](https://tozalionline.com/wp-content/uploads/2022/02/unity-fountain-one.jpg)
Wannan waje ta unity fountain na shimfide ne a unguwar maitama taskiyar millennium park da kuma wannan shahararriyar hotel din mai suna Transcorp Hilton.
Su wannan fountains din wasu gajerun gine gine ne farare da aka ginasu aka kuma katangesu da ‘yar gajeruwar katanga, tare da rubuta sunayen jihohin nigeria guda talatin da shida a jikin wannan ginin. Wannan na nuni da alamun hadin kan wadannan jihohida kuma zaman lafiya a tsakanin mu.
A da can baya a kwai ruwa dake fitowa daka tsakiyar wannan fountain din,yake kwararowa jikin gine ginen gwanin ban sha’awa ,amman yanzu, babu ruwan.
Unity Fountain sanannnen waje ne dake da matukar tasiri a garin Abuja, kuma ake alfahari da wajen , duk da dai yanzu haka,wajen baya samun cikaken kulawa da gyara kamar a da can baya. Mutane da dama na yin kira da gwamnati da su taimaka a dawo da martaban wannan waje ta Unity Fountain.
Daga Maryam Idris