Da Duminsa : Sarauniya Elizabeth II ta mutu, Fadar Buckingham ta sanar

0
165

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu, wacce ta fi dadewa a kan karagar mulki wacce ta shafe shekaru 70 tana mulki, ta rasu ne a ranar Alhamis tana da shekaru 96, in ji fadar Buckingham.

Elizabeth ta hau kan karagar mulki a shekara ta 1952, bayan rasuwar mahaifinta, Sarki George na shida.  Ta lura da tashin hankali na ƙarshe na daular Biritaniya, ta fuskanci tashe-tashen hankula a duniya da abin kunya na cikin gida, kuma ta sabunta tsarin sarauta.

Ta mutu a Balmoral Castle a Scotland bayan likitoci sun ce sun damu da lafiyarta ranar Alhamis.

Elizabeth ta yi sarauta a kan Ƙasar Ingila da wasu ƙasashe 14 na Commonwealth, kuma ta zama ɗaya daga cikin manyan matayen da aka taɓa yi a rayuwa.  An nada Ɗanta, Charles,  Sarki bayan mutuwarta.

By: Firdausi Musa Dantsoho