ECOWAS ta ki amincewa da wa’adin mulkin shekara uku na Nijar

0
26

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta yi watsi da shirin mika mulki ga gwamnatin Nijar na shekaru uku.

Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musah ya bayyana haka yayin wata hira da BBC a ranar Lahadi.

Idan dai za a iya tunawa, shugaban mulkin soja a Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, a ranar Asabar, ya ce zai mika mulki cikin shekaru uku, ya kuma yi gargadin cewa duk wani shiga tsakani da dakarun kasashen waje za su yi, ba zai zama abu mai sauki  ba.

Ya bayyana a wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin ta Tele Sahel, “Burin mu ba shine mu kwace mulki ba. Lokacin canji ba zai wuce shekaru uku ba; a halin da ake ciki, an bukaci jam’iyyun siyasa da su mika ra’ayinsu na mika mulki cikin kwanaki 30.

“Akwai damar yin duk wata tattaunawa, muddin ta yi la’akari da muradin mutanen Nijar. Koyaya, duk wani shiga tsakani zai buɗe hanya ma abubuwa da zasu biyo baya kuma ba zai zama abu mai sauki ba.

Gargadin nasa ya biyo bayan isowar tawagar ECOWAS a kasar domin tattaunawa kafin ta yanke shawarar shiga tsakani na soji a kan mulkin soja.

Sai dai a cikin hirar Musah ya ce dole ne a mika mulki cikin kankanin lokaci.

Ya ce “Ecowas ba za ta sake amincewa da wani tsawaita mika mulki a yankin. Dole ne kawai su shirya don mikawa a cikin mafi kankantar lokaci mai yuwuwa.

“Bangaren soja yana kai sosai”.

“Tun da farko sun ba da mulki ga farar hula tare da mai da hankali kan babban nauyin da ya rataya a wuyansu na kare martabar yankin Nijar, mafi alheri gare su.”

A ranar Asabar ne tsohon shugaban mulkin soji, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd), ya jagoranci tawagar kungiyar ECOWAS zuwa Nijar a wani yunkuri na karshe na diflomasiyya na cimma sulhu da gwamnatin mulkin Nijar.

Tawagar ta gana da firaminista Ali Zeine wanda ya tarbe su a filin tashi da saukar jiragen sama ya kuma kai su fadar shugaban kasa.

Daga baya sun gana da hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum, bayan sun gana da shugaban mulkin soja Janar Abdourahamane Tchiani.

Firdausi Musa Dantsoho