Somaliya ta haramta amfani da TikTok da Telegram

0
42

 

Gwamnatin Somaliya ta haramta amfani da shafukan sada zumunta na TikTok da Telegram, da kuma wata manhajar gasar caca ta yanar gizo, tana mai cewa “‘yan ta’adda” ne ke amfani da su wajen yada farfaganda.

Matakin na zuwa ne gabanin wani mataki na biyu da ake sa ran kaiwa ga farmakin soji a kan kungiyar Al-Shabaab, kungiyar masu kishin Islama da ta yi tada kayar baya a tsakiyar birnin Mogadishu fiye da shekaru 15.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ma’aikatar sadarwa da fasaha ta umurci masu samar da intanet da su aiwatar da dokar nan da ranar 24 ga watan Agusta ko kuma su fuskanci hukuncin da ba a bayyana ba.

A wani bangare an karanta cewa, “A wani yunkuri na hanzarta yaki da kawar da ‘yan ta’addan da suka zubar da jinin al’ummar Somaliya, ministan sadarwa da fasaha ya umurci kamfanonin da ke ba da sabis na intanet da su dakatar da amfani da manhajar TikTok, Telegram, da 1XBET. wadanda ‘yan ta’adda da kungiyoyin da ke da alhakin yada fasikanci ke amfani da su wajen yada faifan bidiyo da hotuna da kuma yaudarar al’umma.”

Tun a watan Agustan shekarar da ta gabata ne sojojin kasar suka fara kai farmaki kan kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaeda a tsakiyar kasar Somaliya, tare da hada karfi da karfe da mayakan sa-kai na cikin gida a wani samame da sojojin kasashen Afirka ke marawa baya da kuma hare-haren jiragen sama na Amurka.

Duk da hare-haren da gwamnatin kasar ke kai wa, har yanzu mayakan na al-Shabaab na rike da yankuna da dama na yankunan karkara, suna kuma ci gaba da kai munanan hare-hare kan fararen hula, da siyasa, da na sojoji.

Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya sha alwashin kawar da masu jihadi a yankin kusurwar Afirka da ke da tashe-tashen hankula, kuma nan ba da jimawa ba za a sanar da kashi na biyu na harin da aka kai musu a kudancin Somaliya.

Firdausi Musa Dantsoho