Gwamnan Gombe ya bi sahun Ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas inda suke Taro karo Na 10 a Bauchi

0
17

Gwamna Inuwa Yahaya Yana Halartar Taron Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Maso Gabas Karo Na Goma A Bauchi

Daga Yunusa Isah kumo

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya ziyarci Bauchi don Halartar Taron Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Maso Gabas (NEGF) karo na 10 tare da takwarorinsa na jihohin yanki.

Taron wadda Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ke jagoranta, wani dandali ne da Gwamnonin yankin ke musayar ra’ayi kan dabarun lalubo ingantattun hanyoyin magance matsalolin dake addabar yankin na Arewa maso Gabas don inganta rayuwar mazauna yankin.

A jawabinsa na buɗe taron, Gwamna Zulum ya jaddada aniyar Gwamnonin yankin na Arewa maso Gabas wajen tinkarar ƙalubalen dake addabar shiyyar.

Ya jaddada muhimmancin magance matsalar rashin tsaro, da koma bayan ilimi, da naƙasun ababen more rayuwa, tare da samar da hanyoyin sauƙaƙa ci gaban tattalin arziƙi da zamantakewa a yankin.

Gwamna Mai masauƙin baƙi Sanata Bala Mohammed, ya bayyana muhimmancin tarukan ƙungiyar akai-akai, yana mai cewa gwamnonin sun himmatu wajen tabbatar da haɗin kan shiyyar da magance matsalolin da yankin ke fuskanta.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana ƙudurin gwamnonin na yin haɗin gwiwa don sauƙe amanar da al’ummar jihohinsu suka ɗora musu.

Ana sa ran fitar da sanarwa a ƙarshen taron.

A yayin buɗe taron, Gwamnonin sun yi amfani da wannan damar wajen ƙaddamar da bikin baje kolin kasuwanci na haɗin gwiwa na shiyyar Arewa maso Gabas wato NACCIMA 2024, gabanin ƙaddamar da kasuwar baje kolin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai yi a gobe a dandalin IBB dake Bauchi.

Ismaila Uba Misilli

Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe.

 

Hafsat Ibrahim