Gwamnatin Buhari Ta Bude Gadar Neja ta Biyu Na Tsawon Kwanaki 30

0
61

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ce za a bude gadar Neja ta biyu na tsawon wata guda.

Naija News ta rahoto cewa Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ne ya bayyana haka a ranar Laraba a wajen kaddamar da gadar.

Fashola ya tabbatar da cewa, gadar wadda aka bude a hukumance a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba domin saukaka zirga-zirga a yankin Kudu maso Gabas a lokacin bukukuwa, za a rufe ta ne a ranar 15 ga watan Janairun 2023. Ministan ya bukaci masu ababen hawa da ke tuki a kan gadar da su yi tuki hankali, su kuma guji yin tukin ganganci domin kada a dakatar da manufar aikin. Da yake jawabi a wajen kaddamar da gadar, Fashola ya ce manufar Shugaba Muhammadu Buhari na kammala gadar ita ce ceton rayuka da kuma rage radadin talauci da bata gari ke haifarwa a kan tsohuwar gadar Neja ta farko. Fashola ya ce bude gadar Neja ta biyu zai rage radadin matafiya wadanda a kodayaushe sukan fuskanci cunkoson ababen hawa a lokacin yuletide. Ya ce: “Mutane da yawa sun yi magana kan mafita amma gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yanke shawarar gina wata gadar domin samun mafita . Don haka, an samu kuɗaɗen ne, daga kuɗin zuba jari, daga kadarorinmu na mai, da wasu kuɗaɗen da aka dawo da su wadda aka sace daga Nijeriya zuwa Amurka. “Sakamakon shine yanzu abin da muke gani.

Gadar zai kasance a buɗe don zirga-zirga daga Yamma zuwa Gabas daga 15 ga Disamba 2022 zuwa 15 ga Janairu 2023. “Ba mu gama aikin ginin gadar ba amma za mu bude ta don mutane su yi amfani da su don rage matsi daga gada daya.

A ranar 15 ga Janairu, 2023, za mu sauya wannan yunkuri na wadanda ke zuwa daga gabas zuwa yamma.”

Daga:Firdausi Musa Dantsoho