Da Duminsa: Jakadan Najeriya a kasar Spain, Demola Seriki ya rasu

0
38

Rahotanni da ke fitowa a safiyar ranar Alhamis sun tabbatar da cewa jakadan Najeriya a kasar Spain, Demola Seriki, ya rasu. Naija News ta fahimci cewa an tabbatar da rasuwar Seriki ga manema labarai a wata sanarwa mai dauke da sa hannun ‘ya’yansa a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce ya rasu ne a birnin Madrid na kasar Spain da sanyin safiyar ranar.

Daga : Firdausi Musa Dantsoho