Gwamnatin Jihar Abia Ta Hana Zirga Zirgan Babur A Aba, Umuahia

0
28

Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bayar da umarnin hana zirga-zirgar masu tuka babura da aka fi sani da okada a cikin garin Umuahia da Aba.

A cewar babban sakataren yada labaran gwamna Otti, Kazie Uko, wannan umarni ya fara aiki nan take.

Sanarwar ta kara da cewa “Gwamnan jihar Abia, Dr. Alex Otti, OFR, ya bayar da umarnin hana zirga-zirgar babura ‘yan kasuwa, wanda aka fi sani da Okada, a cikin Umuahia, babban birnin jihar, da Aba Metropolis.”

“Daga ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, 2023, duk wani babur da aka gani a kan titunan garin Umuahia da Aba da ake amfani da shi don haka jami’an tsaro za su kama shi.

“Har ila yau, an umurci hukumomin tsaro da su kama duk wani mutum da aka kama yana karya wannan umarni, don yuwuwar gurfanar da shi gaban kuliya. Wannan umarnin yana aiki nan take.”

Firdausi Musa Dantsoho