Uwargidan shugaban kasa ta karbi bakuncin Yan Wasan Super Falcons a Aso Rock

0
8

Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, a halin yanzu tana karbar bakuncin ‘yan kungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya, Super Falcons, a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa, Abuja.

Super Falcons ta fice daga gasar cin kofin duniya ta mata na FIFA da ake ci gaba da yi, wanda Australia da New Zealand ke shiryawa, bayan da ta sha kashi a bugun fenareti a hannun tawagar Ingila, a ranar Litinin da ta gabata, 7 ga watan Agusta.

Uwargidan shugaban kasar, wacce ta yi irin wannan ganawa da kungiyar kwallon kwando ta Najeriya, D’Tigresses, wacce ta lashe gasar a ranar Litinin din da ta gabata, tun a ranar Litinin din da ta gabata ta kara karfafa gwiwar mata masu sha’awar wasannin Najeriya ta hanyar jan hankalinsu da gudanar da tarurruka kamar haka.

Firdausi Musa Dantsoho