HANYOYI NA GIDA DA ZAMU BI WAJEN DAINA MUNSHARI A LOKACIN BACCI

0
115

Munshari yana faruwa ne a lokacin da iska ke gudana ta makogwaro lokacin da kuke shaƙan iska a cikin barcinku. Wanda yake saka sinadaran jikinku na makogwaron ya dinga rawa, wanda ke haifar da sauti masu tsauri, mai yuwuwa masu ban haushi da ake kira da munshari.

Munshari na iya damunku a lokacin barcinku haka zalika ma ga abokan zamanku. Ko da ba ya damu da yawa, munshari ba alama ce da za a yi watsi da ita ba.Bisa ga binciken likitoci sun nuna cewa a zahiri, abubuwan da ke jawo munshari wadda kan  iya nuna mummunan yanayi ga  lafiya, ya hada da:

  • obstructive sleep apnea (OSA), wadda yake toshe hanyoyin iska
  • matsala tare da tsarin bakinka, hancinka, ko makogwaro.
  • rashin samun isashshen bacci.

ABUBUWAN DA ZAMUYI AMFANI DASU WAJEN GUJEWA MATSALAN MUNSHARI NA GIDA

  1. Barci a gefe daya.    

Barci akan bayanka wani lokaci yana sa harshenka ya motsa zuwa bayan makogwaro, wanda wani bangare yake toshe iska ta makogwaro hakan kan jawo munshari, amma in ka kwanta ta gefe daya zaka iya kaucewa yin munshari da dare.

  1. Samun isasshen bacci

Ka tabbatar da cewa kan sami isashshen bacci na akalla sa’o’i 7-9 a kowane dare, Rashin barci na iya ƙara haɗarin yin munshari. Wannan saboda yana iya haifar da tsokoki na makogwaro.

  1. ku yawaita daga kan gadon ku

Ɗaga kan gadon ku da ‘yan inci kaɗan na iya taimakawa wajen rage munshari ta hanyar buɗe hanyoyin iska. Kuna iya amfani da samfura kamar masu hawan gado ko matashin kai don samun ɗan tsayi kaɗan.

  1. A guje wa barasa kafin kwanciya barci

Ayi ƙoƙarin kada ku sha barasa aƙalla awanni 3 kafin lokacin kwanciya barci. Barasa na iya kwantar da tsokoki na makogwaro, yana haifar da munshari.

  1. Yawan Kula da matsakaicin nauyi

Idan kana da kiba, rage nauyi zai taimaka wajen rage adadin nama a cikin makogwaro. Yawan nama zai iya haifar da munshari.Haka zalika idan har duka waennan abubuwa da na lissafo basu daina ba sai a tuntubi likita.

BY:UMMU KHULTUM ABDULKADIR