Ministan baban birnin Tarayya Abuja Bar.Nyesome wike ya Mika sakon gaisuwar Ista na musamman ga mazauna babban birnin.

0
16

inistan Babban Birnin Tarayya Abuja,amadadin hukumar babban birnin tarayya Abuja, ya mika sakon gaisuwa ga daukacin mazauna babban birnin tarayya, musamman mabiya addinin kirista bisa wannan buki na murnar Easter.

Ministan ya ce ,al’umma su yi anfani da wannan dama wurin nuna yafiya da tausaya wa juna.

Ya kara da cewa,wannan shine Dama da ya kamata ayi anfani da shi domin taimakawa mabuqata, mu ba da taimako ga masu karamin kari.

Ya ce Allah Ya Albarkaci babban birnin tarayya, da al’umma daban-daban,ya ce al’ada, addini, ko asalinmu ba shine ba,illa hakuri da mutuntadiya ta musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR bisa kyakkyawan jagoranci da jajircewarsa na ci gaban kasarmu Najeriya.

Karkashin ja-gorancinsa, mun shiga tafiya ta canji, ta hanyar sabon bege da kyakkyawan fata. A matsayinmu na mazauna babban birnin tarayya, mu ci gaba da yin imani da Allah da Kuma kya wawan kudurin Shugaba Tinubu da gwamnatinsa, kuma mu ba da gudummawa sosai wajen ganin an cimma burinsa na inganta Nijeriya.

A na mu bangaren, hukumar babban birnin tarayya Abuja ta jajirce wajen tabbatar da walwala da jin dadin duk mazauna. Muna aiki tukuru don magance matsalolin da ke addabar yankin, tun daga tsaro zuwa samar da ababen more rayuwa da ilimi gami da samar da kiwon lafiya.

Don haka ina kira ga kowa da kowa da mu hada hannu da gwamnati wajen neman ci gaba Mu yi aiki tare don gina kyakkyawar makoma ga kanmu da Kuma kasar mu ta gado.

Kamar yadda ake Bikin Ista a yau Ina ma kowa barka da wannan rana in ji shi.

 

Daga Fatima Abubakar.