An kubutar da daliban makarantar Kuriga da ke Jihar kaduna .

0
53

‘Yan bindiga sun sako ‘yan makarantar Kuriga da aka sace a jihar Kaduna.

Gwamnan jihar, Sanata Uba Sani, ya sanar da sakin su a shafin sa na Facebook da aka tabbatar a safiyar Lahadi ta yau 24 ga watan Maris.

Tozali Tv ta tattaro cewa a ranar Alhamis, 8 ga watan Maris, ‘yan bindiga sun sace dalibai sama da 200 a wata makaranta a garin Kuriga dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, inda suka shiga da su daji.

Gwamnan dai bai yi cikakken bayani kan sakin nasu ba, sai dai ya yabawa shugaba Bola Ahmed Tinubu da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu da kuma rundunar sojojin Najeriya.

Gwamnan Ya rubuta cewa, “Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, ina sanar da cewa an sako yaranmu na makarantar Kuriga.

“Muna godiya ta musamman ga mai girma shugaban mu, Bola Ahmed Tinubu, GCFR kan yadda ya ba da fifiko kan tsaro da tsaron ‘yan Nijeriya da kuma tabbatar da ganin an sako yaran makarantar Kuriga da aka sace ba tare da wani lahani ba.

“Yayin da yaran makarantar ke tsare, na yi magana da Shugaban kasar sau da yawa. Ya jajanta mana kuma yana aiki dare da rana tare da mu don tabbatar da dawowar yaran lafiya.

“Sani ya ce Dole ne kuma a yabawa mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Mal. Nuhu Ribadu bisa jagoranci nagari, tare da daidaita ayyukan hukumomin tsaro, wanda a karshe ya haifar da wannan nasara.

“Sojojin Najeriya kuma sun cancanci yabo na musamman don nuna cewa tare da  jajircewa Kan lamarin.

“Muna kuma gode wa daukacin ‘yan Najeriya da suka yi addu’a ga Allah da Ya mayar da yaran makarantar lafiya. Lallai wannan ranar farin ciki ce. Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki.”

A kwanakin baya ne Ministan Tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya bayar da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a kubutar da daliban Kuriga da aka yi garkuwa da su.

Ministan ya bayyana haka ne a Kaduna ranar Alhamis a lokacin da yake jawabi ga sojojin shiyya ta 1 na sojojin Najeriya, wadanda ke a fagen yaki da ‘yan bindiga da ke addabar jihohin Arewa maso Yamma na kasar a lokacin da ya kai musu ziyara domin karfafa musu gwiwa.

“Muna da iko, da niyya, da karfin gwiwa da jajircewa kuma muna da kwarin gwiwa wajen kawo karshen rashin tsaro, na san abin da kuke yi na kubutar da ‘yan makarantar ba tare da jin rauni ba, ku ci gaba da kara kuzari, Shugaban kasa yana bayanku dari bisa dari.

“An sanar da ni kokarin ku na kubutar da yaran makarantar da aka sace. Dabarun da aka yi mini bayani a kai suna tafiya sosai kuma na tabbata za ku same su.

 

Daga Fatima Abubakar.