Hare-hare a ofisoshin INEC ba zai hana zaben 2023 ba – Yakubu

0
35

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a ranar Litinin, ta ba da tabbacin cewa hare-haren da ake kai wa cibiyoyinta ba zai hana gudanar da zaben 2023 ba.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayar da wannan tabbacin a wani taro da kungiyar Tarayyar Afirka na musamman gabanin zabe a karkashin jagorancin Phumzile Mlambo-Ngcuka.

 

 Yakubu ya ce duk da an lalata wasu kayayyakin zabe a hare-haren, hukumar za ta maye gurbinsu.

 

 A cikin makonni uku da suka gabata ne aka kai hari kan ofisoshin kananan hukumomi uku a fadin kasar nan; na baya-bayan nan shi ne ranar Lahadi a Ebonyi.

 

 Ya ce, “Ya zuwa yanzu, za mu iya murmurewa daga duk asarar da aka yi amma abin damuwa ne. Bai kamata a bar wannan ya ci gaba ba.”

Daga :Firdausi Musa Dantsoho