Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ba da beli ga tsohon Gwamnar jahar Anambra Mr Willie Obiano bayan ya shafe mako daya a tsare.
An kama Obiano ne sa’o’i kadan bayan ya mika kujerar sa ga magajin sa farfesa Chukuma Soludo a ranar Alhamis a filin jirgin saman Legas akan hanyar sa ta zuwa Houston ta kasar Amurka.
A larabar da ta gabata ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayar da belin tsohon Gwamnar a lokacin da ya cika sharrudan sa na samun beli.
Sharrudan belin nasa ya hada da karbe masa fasfo.Obiano na tsare ne a bisa zargin karkatar da naira biliyan 42 mallakar jahar ta Anambra.
Da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma da suka hada da naira biliyan 5 na SURE-P da biliyan 37 na jami’an tsaro da aka cire cikin kudin domin gudanar da harkokin siyasar jahar.
Shugaban kafafen yada labarai na EFCC Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan.
By Fatima Abubakar