Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana kudirin sa na tsayawa takaran Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP.

0
120

A jiya 23 ga watan maris 2022,tsohon Shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa,ya yanki tikitin tsayawa takaran Shugaban kasa a karkashin Jamm’iyar PDP wanda kungiyar yan kasuwan Arewa Maso gabas su ka sai masa a kwanan baya.

A jawaban sa ,Atiku ya jaddada niyar sa kuma ya yi alkawari idan har ‘yan Najeriya sun ba shi dama toh zai tabbatar da ya hada kan yan Najeriya a matsayin tsintsiya madaurin ki daya.

Tsohon Mataimakin Shugaban dai ya zargi Gwamnati mai ci da rauni wurin bunkasa jami’an tsaron,tattalin arziki da kuma rarrabuwar kai ga yan Nijeriya.

Ya kara da cewa,shi baya ganin dan Najeriya a matsayin daban-daban  a wurin sa ko daga wace kabila ka fito a dan Najeriya yake kallon Ka.

Kuma yayi alkawarin bada mulki ga matasa bayan ya gama shekarun sa.

An yi taron ne a babban dakin taro na kasa da kasa wato International conference centre (ICC).Taron ya samu halaccin manya-manyan yan siyasa daga wurare daban-daban.

By Fatima Abubakar