Ina Fatan In Ga Dana Wata Rana Inji Mai Shekaru 82 Mahaifin Wadda Ya So Tayar Da Bam A Shekara Ta 2009 Umar Farouk

0
317

Hamshakin attajirin dan kasuwa mai shekaru 82, kuma tsohon shugaban First Bank PLC da UBA, Alhaji Umaru Abdul Mutallab, ya ce yana fatan ganin dansa Farouk Abdul Mutallab, wanda ke zaman daurin rai da rai a gidan yari na Amurka, bisa laifin aikata ta’addanci, Kafin mutuwarsa.

A lokacin yana da shekaru 23, Farouk da ake kira da “mai harin bam”, yayi yunkurin tayar da bama-baman  da aka boye a cikin rigar sa yayin da yake cikin jirgin Northwest Airlines Flight 253, kan hanyarsa daga Amsterdam zuwa Detroit, Michigan, a ranar Kirsimeti, 2009.

Mutallab yayin da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Trust,  a Kaduna ranar Laraba, ya ce yana tattaunawa da dansa amma a karkashin tsatsauran ka’idojin gidan yari.

A cewarsa, dansa yakan kira sau biyu ko sau uku a wata, ya kara da cewa “bama iya buga masa waya  amma shi yana iya buga mana waya kuma mu yi magana”.

kimanin makonni biyu ko uku da suka wuce, mahaifiyarsa, da yan’uwansa suna tare da shi .

Sun ziyarce shi a karkashin tsastsauran ka’idojin gidan yari amma za mu ci gaba da addu’a ga Allah Madaukakin Sarki.  Watakila wata rana, mu sake ganinsa.  Amma halin da ake ciki  inda aka yanke masa hukuncin daurin zaman yari har karshen rayuwarsa sau uku da kuma shekaru 40.  Yana da yawa.”

Amma Allah Madaukakin Sarki ne kadai zai kawo mu cikin yanayin da zamu  gansa a duniya tare da ‘yan uwansa a nan Najeriya,” ya kara da cewa

  BY: Firdausi Musa Dantsoho