Kannywood: Nafisa Abdullahi na daya daga cikin manyan binciken da ake yi a Google a shekarar ta 2021

0
59

Jaruman cikin shirin fim din Labarina ta shiga sahun fitattun jaruman Nollywood na kudancin Najeriya, Destiny Etiko, Tonto Dikeh da Zubby Michael.

Ita ce ta shida a rukunin taurarin fim bayan Destiny Etiko, Zubby Michael, Pere, Tonto Dikeh, Iyabo Ojo da kuma Olu Jacobs.

Haka kuma, Nafisa ita ce tauraruwar Kannywood daya tilo da ta samu matsayi na 10 a fagen bincike na Google.

Sai kuma Rahama Sadau, Fati Washa, Maryam Yahaya da Hadiza Gabon da Ke biye da ita.

Amfani da Google na karuwa akai-akai tun ranar daya.

Har ila yau, shafin yana da sunan rukuni, tare da ƙungiyar mawaƙa da waƙa da kanta da wasanni da ƴan wasan kwaikwayo da kuma fina-finai da kansu tare da tambayoyin da aka fi yawan yi.

Nafisa tana da mabiya fiye da miliyan biyu a Instagram da 176,600 a Twitter da kuma wasu miliyan biyu a Facebook.

Kamar yadda bayanai suka nuna, Nafisa ta fara shahara ne a shafin daga ranar 3 zuwa 9 ga watan Janairun 2021.

 Hakan dai bai rasa nasaba da kammala kashi na biyu na fim dinta da aka dade ana yi ba, wanda zai fara fitowa a karshen watan Disambar 2020.

 

 Neman Tauraron ya karu zuwa kashi 93 cikin 100 a watan Satumba, a daidai lokacin da shirin Labarina karo na 3 ya kasance.

 

 Bugu da kari, manazarta Nafisa Abdullahi ta karu zuwa kashi 100 daga ranar 5 ga watan Disamba zuwa 11. Idan kuma ba ku manta ba, yana da alaka da kayan kwalliyar da NAFCOSMETICS ta kaddamar.

 Mazauna Abuja babban birnin Najeriya ne suka fi neman Jaruma Nafisa ruwa a jallo   sai kuma Rivers da Legas da kuma Kaduna

Shekara biyu kenan ba a kara ganin Nafisa Abdullahi a harkar fim ba kafin ta fara fitowa a cikin shirin fim na Labarina a shekarar 2020.

 

 Fim din wanda Aminu Saira na Saira Movies ne ya bada umarni, Nafisa ta taka rawa a matsayin jarumar da labarin ya taso a kanta.

 

 Tun bayan fitowar Labarina ba a samu wani fim da Nafisa ta fito a ciki ba wanda ya kusa shaharar Labarina.

 

 Yayin da tauraruwarta ke haskawa, ta kaddamar da sabon kamfaninta na kayan kwalliya na Nafcosmetics a watan Nuwamba 2021.

 

 Bugu da kari, tauraruwar ta shahara da tafiye-tafiye zuwa kasashen Turai da Amurka, inda take zuwa neman karin karatu ko yawon bude ido.

 

By: Firdausi Musa Dantsoho

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here