Jahar Nasarawa ta rufe makarantun ta na Gwamnati har ma da masu zaman kan su.

0
52

Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayar da umarnin rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar nan take saboda barazanar tsaro.

Kwamishiniyar ilimi ta jihar Fatu Jimita Sabo ce ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar a ranar Laraba a garin Lafia babban birnin jihar.

Fatu ta ce, bayan majalisar ta yi nazari a kan yanayin tsaro da ake fama da shi a jihar da ma kasar nan, musamman kan matsalar tsaro a babban birnin tarayya Abuja, gwamnatin jihar ta yanke shawarar rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar nan take.

Ta kara da cewa, ya zama wajibi idan aka yi la’akari da kusancin jihar da babban birnin tarayya Abuja, da kuma kudurin gwamnati na ganin cewa makarantun jihar Nasarawa suna gudanar da ayyukansu cikin yanayi mai kyau.

Sai dai ta bayyana cewa umarnin ya kebanta da azuzuwan fita da tuni suka fara rubuta jarabawar karshe, musamman a makarantun sakandare.

Sai dai ta yi kira ga iyaye da kada su firgita, inda ta kara da cewa jihar Nasarawa tana nan lafiya amma an dauki matakin ne a matsayin wani mataki na kare rayukan yara da dalibai a fadin jihar.

Haka zalika Hajiya Sabo ta yi kira ga shuwagabannin makarantu da su tabbatar da cewa an rufe makarantun cikin tsari, musamman babu wata barazana ga rayuwa ko dukiya a halin yanzu a jihar Nasarawa.

Daga Fatima Abubakar.