Jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta koka kan shirin da gwamnati mai mulki ke yi na muzgunawa tare da kame mambobinta.
Idan ba a manta ba, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsayar da ranar Asabar 15 ga watan Afrilu domin gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya da na ‘yan majalisar jiha a fadin kasar nan. Za a sake zaben Sanatan Zamfara ta tsakiya da kujeru biyu na majalisar wakilai.
A wata sanarwa da ofishin yada labarai na Dauda Lawal ya fitar a ranar Laraba a Gusau, jam’iyyar ta nuna damuwarta kan katsalandan da ake zargin babban sufeton yan Sandan ya yi.
Jam’iyyar ta kuma ce gwamnan yana anfani da abokantakarsa da Sufeto Janar na ‘yan sanda wajen kulla makarkashiyar kamawa da kuma tursasa wasu manyan ‘yan PDP.
Sanarwar ta kara da cewa: “Mun damu matuka da mugun nufin gwamnan jihar Zamfara mai barin gado, Bello Matawalle, na sanya siyasa a harkokin ‘yan sandan Najeriya ta hanyar amfani da alaka da abokantakarsa da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba…”
“Idan akwai wanda ya bukaci a kama shi da laifin aikata laifukan zabe, mun yi imanin cewa gwamna mai barin gado, da mataimakansa, da ‘yan sandan gidan gwamnati ya kamata su kasance kan gaba a jerin sunayen.
“A kan wannan batu, muna so mu kada kuri’ar rashin amincewa da babban sufeto Janar na ‘yan sanda saboda katsalandan da yake yi a siyasar Zamfara. Dokar ta bayyana sarai yadda wadanda suka fusata ko wadanda suka sha kaye a zabe za su gabatar da kokensu. Rundunar ‘yan sandan Najeriya ba ta da alaka da shari’o’in zaben da za a gudanar ko bayan zabe.
“Abin mamakinmu, manyan shugabannin jam’iyyar PDP na Zamfara sun samu takardar gayyata daga ofishin babban sufeton ‘yan sanda na kasa kan zargin da ake yi na yin magudi a zaben 2023.
“Wannan shi ne kololuwar rashin sanin makamar aiki da Sufeto Janar na ‘yan sanda ke nunawa, kuma mun fusata da shi. Mun yi imanin cewa gayyatar wani mataki ne… don muzgunawa da kuma tsoratar da ’yan jam’iyyar PDP na Zamfara don hana su shiga zaben da za a sake yi a ranar Asabar, 15 ga Afrilu.
“Muna kara kira ga jama’a da su san halin da ake ciki a Zamfara da kuma yiyuwar amfani da ‘yan sanda wajen murkushe shugabannin jam’iyyar mu, musamman ma ga kawo cikas ga sake zaben ranar Asabar. Suna da cikakkiyar masaniyar cewa PDP ce za ta lashe majalisar dattawa ta tsakiya da sauran kujeru biyu na wakilai, don haka suna kan gaba don kokarin haifar da rikici.
“Daga cikin shugabannin PDP da Sufeto Janar na ‘yan sanda ya gayyace su ba bisa ka’ida ba, akwai Alhaji Garba Ahmad Yandi, Alhaji Kabiru Ahmadu; Alhaji Yusuf Daha Tsafe; Alhaji Ibrahim Modibbo; Alhaji Zahradeen Ibrahim; Alhaji Musa Malaha; Alhaji Sambo A. Sambo; Hajiya Lubnah Baba Gusau da sauran su.
“Mutanen da aka kai wa harin, shugabannin jam’iyyar ne daga yankunan da abin ya shafa inda za a sake zaben ranar Asabar. Hakan ya kara fallasa sirrin manufar shugaban ‘yan sandan Najeriya.
“Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kira babban sufeton ‘yan sanda ya ba da umarni. Muna kuma kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da masu sa ido na kasa da kasa da su sanya ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a jihar Zamfara.
Daga Fatima Abubakar.