Zababben dan majalisar wakilai a mazabar Chibok a jihar Borno ya rasu.

0
28

Nuhu Clark, zababben dan majalisar wakilai na mazabar Chibok a majalisar dokokin Borno ya rasu.

An ruwaito cewa Clark, wanda ke karbar magani a Indiya, ya mutu ranar Litinin.

An gudanar da zaben majalisar dokokin jihar tare da zaben gwamna a ranar 18 ga watan Maris.Clark ya rasu kwanaki 23 da gudanar da zaben.

Kwamishinan harkokin cikin gida, yada labarai da al’adu na jihar, Babakura Abbajatau, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da aka yi da shi a yau Laraba.

Umar Kadafur mataimakin gwamnan jihar yace wannan rashi ne ga iyalansa da mutanen kudancin Borno da ma jihar baki daya.

Kadafur, yayin da yake jajantawa iyalan marigayin, ya bayyana rasuwar Clark a matsayin rashi ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), inda ya kara da cewa marigayin dan siyasar ya taimaka wajen ci gaban jihar.

Clark ya kasance tsohon kwamishinan yaki da fatara ne a Borno.

An ce ya yi murabus daga mukaminsa na kwamishinan da zai tsaya takarar mazabar Chibok a karkashin jam’iyyar APC.

 

Daga Fatima Abubakar.