Kamfanin sufuri na CIDDESS ya shirya tattakin wayar da kan jama’a a Abuja, domin fara amfani Manhajarsa.
Shirin na wayar da Kan Al umma Kan amfani da manhajar an shiryashi ne don bayyana manufofin kamfanin Wanda yake da sauki ga masu amfani da abin hawa na haya, musamman don biyan bukatar kwastomomin, ta hanyar zuwa inda kakeso akan lokaci .
Suma masu motoci wato direbobi ba a barsu a baya ba inda kamfanin ya Basu tagomashin yin aiki kafada da kafada dasu, domin biyan bukatan daidaikun mutane ko Taron jama a.
Tattakin sun Farashi daga office dinsu dake kallon gidan breading cash and carry Jahi layin Nipcon ground . Inda suka nufi guraren da Jama a ke hada hada don jin dadin al umma ciki kuwa hadda kasuwar banex, daga Nan sai suka nufi kasuwar wuse ,inda nan ma suka wayar da Jama a Kan Muhimmancin manhajar ta ciddess ga harkokin zirga- zirgar yau da kullum
Kasauke manhajar wacce taka aiki awa24 don biyan bukatar Al umma tare da saukaka musu .
Daga Nan suka qarasa cediq plaza, dadai sauransu Muhimmanci wajeje a cikin birnin tarayyar.
Anasa bangaren Mr Ishola David Mayokun Ya bayyana makasudun kamfanin Wanda yayi rahusa ga mutanan farko wadanda suka fara yin amfani dasu, inda yace akwai rahusa na ragin kaso 20% ciki 100 .
Daga karshe yayi qarin bayani Kan Amfanin manhajar Ciddess app” shine manhajar data baiwa Yan Nageriya sauki ta ko wanne hali wanda zai dinga karfafawa masu hada – hadarsu tare da Basu damar yin zirga-zirga cikin sauki ba tare da damuwa ba. Manufarmu itace saukaka sufiri da Kuma yin rangwame musamman direbobi . Wanda ba zai Shafi albashin suba wato tagomashi ne nasu Sannan za su karbi albashin su a karshen wata. Mun gano cewa yawancin direbobi ba su da wani tanadi bayan sun sayi man fetur ko gyara motocinsu, hakan yasa muka saukaka musu. Ciddess yabawa ko wannan addini damar sa aduk lokacin ibada bamuyin aiki, kuma ana samunmu a koda yaushe .
Mun shirya tsaf don farantawa Al umma da Kuma Kare dukiyoyinsu. Don saukakawa ma abota amfani da manhajar.
Hafsat Ibrahim