Majalisar Dokokin jihar kano ta rushe dokar kafa Masarautu biyar

0
17

Majalisar Dokokin jihar kano ta rushe dokar kafa Masarautu biyar da aka yi tare da maye gurbinta da sabuwar dokar marautar kano guda daya kamar yanda take tun asalin tarihin kasuwar Masarautar shekaru dari tara da casa’in da tara da suka shude a zamanin Shehu Usman Danfodiyo.

 

Mataimakin shugaban majalisar kuma Wakilin kananan hukumomin Rimin Gado da Tofa Rt. Hon. Mohammad Bello Butu-Butu ne ya gabatar da dokar a zaman Majalisar na yau.

 

Da yake karin haske akan sabuwar dokar Shugaban masu rinjaye kuma Wakilin karamar Hukumar Dala Alh. Lawan Hussaini Chediyar ‘Yan Gurasa ya ce sabuwar dokar za ta tabbatar da dorawar tarihi da martabar kuma darajar Masarautar tare da bunkasarta da kuma inganta tsaro da cigaban jahar kano.

 

Shugaban masu rinjayen ya cigaba da cewa da zarar gwamna ya saka hannu a dokar zai iya nada sababbin ‘yan majalisar Sarki wadanda za su zabi sabon Sarkin Kano.

 

Sai dai mai tsawatarwa marasa rinjaye kuma Wakilin karamar Hukumar Kabo a Majalisar Hon. Ayuba Labaran Durum da takwaransa na Bichi dana Gabasawa sun fice bisa nuna rashin gamsuwarsu akan dokar rushe masarautun guda hudu,

 

Majalisar ta dage zamanta zuwa gobe Juma’a 24 ga watan Mayun 2024 wanda ya zo dai-dai da 16 ga watan Zhul-khada hijirah 1445.

 

 

 

Hafsat Ibrahim