Majalisar Wakilai Ta Fara Tantance Shugabannin Hafsoshin Tsaro

0
17

A yau Litinin ne majalisar wakilai ta fara tantance shugabanin hafsoshin tsaro da shugaba Bola Tinubu ya nada a kwanakin baya.

Kwamitin tantancewar ya kasance karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar, Julius Ihonvbere.

Hafsan hafsoshin sun hada da Manjo Janar Christopher Musa (shugaban hafsan tsaron kasa), Manjo Janar Taoreed Lagbaja (shugaban rundunar soji), Rear Admiral Emmanuel Ogalla (shugaban sojojin ruwa), da AVM Hassan Abubakar (shugaban hafsan sojin sama).

Shugaban Kwamitin Adhoc na Majalisar, Babajimi Benson, ya ce dole ne ‘yan rundunar soji su bi ka’idojin da dokar kasa ta tanada, ya kuma bukace su da su yi aiki tare ta hanyar musayar bayanan sirri.

Ya ci gaba da cewa ayyukan shugabannin ma’aikatan majalisar dokokin kasar za su duba su idan an tabbatar da su.

Manjo Janar Musa ya sha alwashin cewa a karkashin sa sojojin za su kare martabar yankunan kasar da kuma yin aiki tare.

Zaman ya biyo bayan tantancewa tare da tabbatar da nadin shugabannin hukumar da majalisar ta yi a ranar Alhamis din da ta gabata.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce hafsoshin tsaron sun amsa tambayoyi kan batutuwan da suka shafi tsaro da kuma batutuwan daban daban a yayin zaman da suka yi na sirri.

A ranar 19 ga watan Yunin 2023, makwanni uku kenan da rantsar da shi, Tinubu ya tsige shugabannin hafsoshin tsaro a Najeriya tare da nada sabbi wadanda ya umurce su da su ci gaba da aiki nan take.

Wadanda abin ya shafa sun hada da Alkali Usman wanda aka tsige shi daga mukamin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Lucky Irabor, wanda aka kora daga mukamin babban hafsan tsaron kasa; Faruk Yahaya, ya yi ritaya a matsayin babban hafsan soji; Awwal Gambo, wanda aka tsige a matsayin hafsan hafsoshin ruwa; da Isiaka Amao, mai ritaya a matsayin babban hafsan hafsoshin sojin sama.

Daga nan ne shugaban ya nada sabbin hafsoshin tsaro tare da nada tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC Nuhu Ribadu a matsayin sabon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro (NSA). Ribadu ya maye gurbin Babagana Monguno a matsayin NSA na kasa.

Tinubu ya kuma nada Adeniyi Adewale a matsayin mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam.

Tuni dai dukkan sabbin nade-naden da aka nada suka koma bakin aiki kafin majalisar dokokin kasar ta tabbatar da su.

Firdausi Musa Dantsoho