Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar zaman majalisar zartarwa ta tarayya a fadar gwamnati dake Abuja.
Taron na FEC na wannan makon shi ne na farko bayan zaben shugaban kasa da ya samu fitowar jam’iyyar All Progressives Congress Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.
Akwai sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha; Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folashade Yemi-Esan; Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu.
Ministocin da ke halartar taron sun hada da ministocin harkokin jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban al’umma, Sadiya Farouk; Kudi, Zainab Ahmed; Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Niyi Adebayo; Noma, Mohammad Abubakar; Jirgin sama, Hadi Sirika; Niger Delta, Umana Umana; Lantarki,Abubakar Aliyu; Matasa da Wasanni, Lahadi Dare; Sufuri, Mu’azu Sambo da Muhalli, Mohammed Abdullahi.
Haka kuma ministocin kasafi da tsare-tsare na kasa, Clem Agba; Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Mariam Katagum; Kimiyya da Fasaha, Henry Ikoh; Harkokin Waje, Zubairu Dada; Man Fetur, Timipre Sylva.
Daga Fatima Abubakar.