Jam’iyyar APC mai mulki ta ci gaba da rike madafun ikonta na majalisar dattawa.

0
29

Jam’iyyar APC mai mulki ta ci gaba da rike madafun ikonta na majalisar dattawa, inda ta samu kujeru 49, kamar yadda sakamakon zaben ‘yan majalisar dokokin da hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar ya zuwa yanzu.

Daga cikin kujeru 89 da aka sanar kawo yanzu, jam’iyyar PDP ta samu kujeru 28; Labour Party shida yayin da New Nigeria Peoples Party (NNPP) da Social Democratic Party (SDP) suka samu kujeru biyu kowanne.

A halin da ake ciki dai, jam’iyyar Young Progressive Party (YPP) da All Progressives Grand Alliance (APGA) sun samar da sanata daya kacal kowannensu.

Tare da Sanatoci 49, har yanzu jam’iyya mai mulki ta sake tsayawa tsayin daka don samun rinjaye a majalisar dattawa ta 10. Akwai kujeru 109 a cikin Red Chamber, wanda ya ƙunshi kujeru uku a kowace jiha da ɗaya a babban birnin tarayya Abuja.

Jam’iyyar da ke da rinjaye mai sauƙi tana samar da shugabannin da ake kira Shugaban Majalisar Dattawa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

 

Daga Fatima Abubakar.