Ministan Sadarwa Da Tattalin Arziki Na Zamani Farfesa Ali Pantami Ya Kaddamar Da Mambobin Kwamitin Gudanarwa Na NIMC, NIPOST DA NITDA 44.

0
161

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital, Farfesa Isa Pantami ya kaddamar da wasu mambobi 44 na kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Shaida ta Kasa (NIMC), Ma’aikatar Wasikun Najeriya (NIPOST) da Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA).

Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar a Abuja, Pantami ya bukaci mambobin kwamitin da su himmatu wajen aiwatar da manufofin tattalin arziki na dijital.

 Pantami ya ce nauyin da ke wuyan sabbin mambobin hukumar gudanarwar da aka kaddamar shi ne sanya ido da kuma kula da ayyukan hukumomin tare da inganta manufofin kasa da ma’aikatar sa ido ta samar.Ya kara da cewa “Mun kaddamar da mambobin Hukumar Mulki 44, 17 na NIMC tare da tsofaffin jami’an da suka hada da wadanda Shugaban kasa ya nada da sauran su.

A fannin “NITDA muna da mutum 19 da suka hada da shugaba da babban jami’in gudanarwa wanda ke aiki a matsayin sakatare da mambobin, haka kuma hukumar NIPOST tana da mambobi 8. muna fatan za ku ci gaba da nuna kwarewa,” in ji shi.

“Ya kamata ku yi iya ƙoƙarinku a cikin ayyukan da aka ba ku ta hanyar ayyuka daban-daban masu ba da damar kafa wannan tsari da sauran manufofi da umarnin gwamnati waɗanda za su iya fitowa daga lokaci zuwa lokaci.

“Fiye da kashi 90 cikin 100 na wadanda aka nada a yau an sake nada su ne sakamakon shawarwarin da muka bayar da kuma yadda suka nuna jajircewarsu ta hanyar da suke mu’amala da ma’aikata.

Daga cikin wadanda aka sake nadawa a matsayin shugabanni, shugabanmu/MD na fitacciyar tashar Talabijin da Mujallar Tozali, Bar.Maimuna Yaya Abubakar ba a bar ta a baya ba, domin ita ce shugabar Hukumar Nipost.

Ministan sadarwa Farfesa Ali Pantami ya bukace su da su tabbatar sun mutunta ikon tsarin mulki a duk abin da suke yi. Kuma hukumar ba ta da wani iko dangane da bayar da kwangiloli sannan kuma Ministan ma ba shi da iko wajen bayar da kwangiloli a matsayin wani matsayi mai zaman kansa.

“Don yin adalci a gare ku duka. Ina matukar godiya da irin yadda kuke kokarin nuna inganci da kanku ta hanyar aiki bisa tsarin doka da manufofin gwamnati da fatan za ku inganta a wa’adi na biyu,” A cewar minista Pantami.

 UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.