Mutane 7 ne ake fargabar an kashe tare da kwantar da wasu da dama a asibiti bayan sun sha shayin da ake zargin an yi da wani ganyen garin da aka fi sani da Zakami a wajen wani daurin aure a Kano.
Zakami yana ƙunshe da sinadari da ke taba kwakwalwa.
Shedun gani da ido sun ce lamarin ya shafi kusan mutane 50 kuma har yanzu ba a gansu ba. Lamarin ya faru ne a unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso a cikin birnin Kano.
Daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin, Sanusi Yahaya, wanda kuma dan uwa ne ga amaryar, ya ce ana zargin shayin an hada shi ne wasu gayayyaki daban-daban banda ganyen shayin gida.
Ya ce ya zama ruwan dare ga matasan yankin musamman masu shaye-shayen miyagun kwayoyi su rika dafa shayi a lokacin bukukuwa kuma suna fakewa da hakan domin shan kwaya.
“Sun dafa shayin kuma su da kansu ba su san adadi da nau’in magungunan da ke ciki ba har wasu sun yi watsi da shi. Amma wasu daga cikinsu sun dage cewa dole ne su sha shayin, suna masu cewa kwakwalwar su na iya dauka.
“Bayan shan shayin, mutane biyu sun mutu, wasu sun murmure yayin da wasu ke kwance a asibiti,” in ji shi.
Wani shaida Abdullahi Muhammad ya ce ya zuwa ranar Talata mutane bakwai ne suka mutu.
Ya ce wasu daga cikin wadanda ke kwance a asibiti ba ’yan unguwar ba ne amma suna wucewa ne kawai suka yanke shawarar shan shayin.
“Ba mu san ainihin adadin ba a yanzu, amma da safe an tabbatar da mutuwar bakwai. Wasu ma ba a gayyace su zuwa daurin auren ba, sun zo ne domin su yi kwalliya su sha kwaya,” inji shi.
Ba a iya samun angon don jin ta bakinsa game da lamarin ba saboda an ce ya gudu tare da wasu.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura domin ba a samu lambarsa ba.
Har yanzu dai bai amsa sakon da aka aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Firdausi Musa Dantsoho