Nan Ba Da Daɗewa Ba Za Mu Sanya Ranar Zaɓen Ƙananan Hukumomi – Gwamnan Gombe

0
9

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba gwamnatinsa za ta tsaida ranar da za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata liyafar cin abincin dare daya shirya don karrama tsofin shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin jihar 11, biyo bayan ƙarewar wa’adinsu a ranar 31 ga watan Disamban 2023.

Gwamnan yace, “Zabe shine gishirin ƙwaƙƙwarar demokraɗiyya, za mu sanar da ranar da za mu yi zaɓen ƙananan hukumominmu, duk mai sha’awa yana da ‘yancin tsayawa takara”.

Gwamna Inuwa ya bayyana kwarin gwiwar cewa Jam’iyyar APC mai mulki za ta samu nasara a zaɓen, yana mai bugun ƙirjin cewa “Zaɓe ne da muka saba da shi, ba wani sabon abu ba ne, muna da yaƙinin cewa har gobe muna da goyon bayan jama’armu, ba ma tsoron a fita rumfunan zaɓe a buga ko da gobe ne kuwa, za mu samu nasara da yardar Allah”.

Ya kuma yabawa tsofin shugabannin riƙon ƙananan hukumomin bisa yadda suka yiwa jama’a da jiharsu hidima, yana mai tabbatar da cewa har yanzu suna tare uwa ɗaya uba ɗaya.

Yace kafin zuwansa mulki a matsayin gwamna, sai jihar ta karɓo bashin Naira biliyan 1 da miliyan 300 a duk wata kafin ta iya biyan albashin ƙananan hukumomi.

“Amma bisa kula da samar da kyakkyawan tsari, bayan watanni biyu kacal, muka ɗauki matakan kawo ƙarshen wannar matsala, kuma tun daga lokacin, mun ci gaba da biyan albashi akan kari ba tare da karɓo wani bashi ba, a maganar da nake muku yanzu haka, ƙananan hukumominmu suna da abinda bai gaza Naira biliyan 6 da miliyan 200 ba a cikin asusunsu,” in ji gwamnan.

Tun farko a jawabinsa na maraba, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Ci Gaban Al’umma Abdulkadir Muhammad Waziri, ya yabawa tsofin shugabannin riƙon bisa kwazon da suka nuna.

A jawabinsa na godiya a madadin tsofin shugabannin riƙon na ƙananan hukumomi, tsohon shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Akko Hon. Abubakar Barambu ya yabawa gwamna Inuwa Yahaya bisa basu damar yiwa al’ummarsu hidima a wannan matsayi.

Da suke yabawa gwamnan bisa salon jagorancinsa abun misali, tsofin shugabannin sun ba shi tabbacin ci gaba da biyayya da goyon bayansu ga manufofi da tsare-tsaren gwamnatinsa.

A yayin liyafar dai, an bada lambobin yabo ga tsofin shugabannin riƙon don nuna godiya ga hidimar da suka yi.

 

Hafsat Ibrahim