GWAMNAN ZAMFARA YA KADDAMAR DA RABON KAYAN ANFANIN GONA GA MANOMAN KANANAN HUKUMOMIN BUNGUDU DA MARU
A ranar Juma’a ne Gwamna Dauda Lawal ya raba kayan amfanin gona ga manoman kananan hukumomin Bungudu da Maru na jihar Zamfara.
Kaddamar da rabon kayan a Bungudu da Maru, wani bangare ne na ci gaba da shirin farfado da tattalin arziki na COVID-19 wanda FADAMA III ke daukar nauyi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa an fara rabon kayayyakin ne a ranar 3 ga watan Janairu a Gusau birnin jihar.
Ya kara da cewa Gwamna Lawal ya je Shinkafi, Gummi, da Tsafe inda ya kaddamar da rabon kayan ga manoma.
“Yau Gwamnan ya ziyarci kananan hukumomin Bungudu da Maru domin raba muhimman kayayyakin noma da kayan amfanin gona ga manoma.
A karamar hukumar Bungudu, Gwamna Lawal ya ce karamar hukumar ta shahara wajen noma, kuma irin gudunmawar da ta bayar wajen habaka arzikin jihar Zamfara abin a yaba ne. “Tare da kaddamar da wannan shiri a wannan karamar hukumar a yau, muna samar da damammaki masu yawa ga al’ummomin da suke noma a wannan karamar hukumar mai himma.
“Ina da yakinin cewa wannan shiri zai taimaka matuka wajen bunkasa noman manoman mu, ta yadda za a rage radadin talauci da kalubalen da ke tattare da shi.
“Kari kan wannan yunƙurin, muna shirin gabatar da irin wannan ayyukan na cigaban al’ummar mu, kamar haɗaɗɗiyar shirin kasuwanci. Wannan shirin zai kunshi ayyuka daban-daban na hadin gwiwar noma, wadanda suka hada da kifaye, kiwon kaji, da sauran su.
“Bugu da ƙari, za ta ba da horo da fakitin farawa ga ƙananan ƴan kasuwa a sassa daban-daban, wanda zai ba da gudummawa sosai ga ƙoƙarin mu na inganta tattalin arzikinmu.
A karamar hukumar Maru, Gwamnan ya sake bayyana cewa rabon tallafin zai magance zazzabin cizon sauro ta hanyar sabbin hanyoyi kamar kiwon kifin tilapia tare da samar da makudan kudade ga wadanda suka ci gajiyar tallafin ta hanyoyi daban-daban, domin babu shakka hakan yana inganta rayuwa.
“A bisa kudurinmu na inganta noma a karamar hukumar Maru, gwamnatina za ta fara aikin gyaran madatsun ruwa na kasa, kuma an yi tanadin wannan a kasafin kudin 2024. Wannan shiri zai samar da guraben aikin yi ga manoma sama da 40,000 tare da taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da mutane sama da miliyan biyu a duk shekara.”
A yayin kaddamar da wannan aiki, sama da manoma 2,000 ne suka amfana a dukkanin kananan hukumomin Bungudu da Maru.
SULAIMAN BALA IDRIS
Babban mataimaki na musamman (kafafen sadarwa da watsa labarai) ga Gwamnan Zamfara
Fabrairu 02, 2024
Hafsat Ibrahim