CI GABA DA SAMAR DA ABINCI: GWAMNAN ZAMFARA YA KADDAMAR DA RABON KAYAN ANFANIN GONA A KANANAN HUKUMOMIN BIRNIN MAGAJI, ZURMI, DA KAURA NAMODA

0
6

CI GABA DA SAMAR DA ABINCI: GWAMNAN ZAMFARA YA KADDAMAR DA RABON KAYAN ANFANIN GONA A KANANAN HUKUMOMIN BIRNIN MAGAJI, ZURMI, DA KAURA NAMOD

 

A ranar lahadi ne Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar da rabon muhimman kayayyakin amfanin gona ga manoma a kananan hukumomin Birnin Magaji, Zurmi, da Kauran Namoda a jihar Zamfara.

 

Bikin raba kayan noman ci gaba ne bayan soma kaddamar da shirin a wasu kananan hukumomin jihar karkashin shirin farfado da tattalin arziki na COVID-19 a jihar Zamfara karkashin FADAMA III.

 

A wata sanarwa da mai magana da yawun gGwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce sama da kashi 80% na al’ummar Zamfara manoma ne.

 

Ya kara da cewa a karkashin wannan shiri, sama da manoma 100,000 a fadin kananan hukumomin (14) zasu afana da kayan aikin noma da iri a cikin shekaru hudu (4) masu zuwa na wannan gwamnati don iganta noman su.

 

A bisa kudirinsa na tabbatar da samar da abinci a fadin jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya raba muhimman kayayyakin noma ga manoma a kananan hukumomin Birnin Magaji, Zurmi, da Kauran Namoda.

 

A yayin kaddamar da rabon a karamar hukumar Birnin Magaji, Gwamna Lawal ya nanata cewa gwamnatin sa na da burin wayar da kan jama’a game da shirin inganta rayuwar jama’a da ake yi a wasu zababbun kananan hukumomin dake yankin mazabu uku (3) na jihar. “Manufar ita ce ƙarfafawa manoma tare da cimma manufofin da aka tsara don habaka tattalin ariziki acikin al’umma. Wannan yunkuri zai kara habaka noma a karamar hukumar Birnin Magaji.

 

“Sauran muhimman ayyukan da gwamnatina takeyi a karamar hukumar Birnin Magaji sun hada da aikin gyaran makarantar GSS Birnin Magaji, aikin titin da ya taso daga Gidan Bita-Maikosa Mallankara-Dandogo-Gamo-Naniya-Kukoki Kwacho- Birnin Magaji, da aikin titin Birnin Magaji. na titin Dakitakwas- Birnin Magaji, da sauran ayyuka da dama Insha Allahu.”

 

A karamar hukumar Zurmi, Gwamnan ya bukaci wadanda suka ci gajiyar wannan shirin, da su yi amfani da wannan damar ta hanyar da ta dace, don habaka noman su, da inganta rayuwarsu.

 

“Baya ga rabon kayan amfanin gona, karamar hukumar Zurmi za ta ci gajiyar ayyuka da dama a cikin kasafin kudin shekarar 2024. Wadannan ayyuka sun hada da gyara tare da samar da kayan aiki a makarantar GGDSS Zurmi da ake yi, da na babban asibitin garin Zurmi, da ginin titin Zurmi-Rukudawa, da gyaran kotun majistare, da sauran ayyuka da dama Insha Allahu.

 

“Ina so in yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga daukacin al’ummar Karamar Hukumar Zurmi da su bayar da cikakken goyon baya da hadin kai ga jami’an tsaron kariyar jama’a (Askarawan Zamfara) don tabbatar da tsaron al’ummarmu.

 

A lokacin da yake kaddamar da rabon kayayyakin a karamar hukumar Kauran Namoda, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa a matsayinsa na Gwamna jihar Zamfara, jihar za ta samu bunkasar noma da sauran sassan tattalin arzikinmu.

 

“Tare da kaddamar da Askarawa da aka yi a baya-bayan nan, baya ga dimbin matakan da muka aiwatar domin inganta harkar tsaro a fadin jihar, ina fatan manoman da suka kasa noma gonakinsu saboda barazanar ‘yan fashi su koma gonannakin su don cigaba da noman su.

 

“Sauran ayyukan da gwamnatina ta yi a karamar hukumar Kauran Namoda sun hada da gyara tare da samar da kayan aiki a babbar Asibitin Kaura Namoda, ginin kwalejin koyon Shari’a da Addinin musulunci, Kaura Namoda, gina Cibiyar Matasa ta yankin Zamfara ta arewa da kammala aikin gidan gyaran hali, Gina ofishin Ilimi na yankin, Gina cibiyar cigaban Ilimi ta mata, Kaura Namoda, gina ƙarin dakunan shan magani a babbar Asibiti, Gina masarauta, da sauran ayyuka da dama Insha Allahu.”

 

SULAIMAN BALA IDRIS

Babban mataimaki na musamman (kafafen sadarwa da watsa labarai) ga Gwamnan Zamfara

Fabrairu 04, 2024

 

Hafsat Ibrahim