Rahotanni sun bayyana cewa El-Rufai ya janye sha’awar zama Minista

0
18

 

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya janye sha’awar sa na kasancewa cikin majalisar ministocin shugaba Bola Tinubu, PREMIUM TIMES za ta iya kawo rahoto na musamman.

Majiyoyin fadar shugaban kasa sun ce Mista El-Rufai ya shaidawa shugaba Tinubu a wani taro a ranar Talata cewa ba ya sha’awar zama minista amma zai ci gaba da ba da gudummawar kason da ya ke da shi wajen ci gaban Nijeriya a matsayinsa na dan kasa mai zaman kansa.

“Ya kuma gaya wa shugaban cewa yana bukatar lokaci don mayar da hankali kan shirinsa na digiri na uku a wata jami’a a Netherlands,” in ji daya daga cikin majiyoyin mu.

Wani mai sharhi ya kuma shaida wa wannan kafar yada labarai cewa tsohon gwamnan ya ba da shawarar a nada Jafaru Ibrahim Sani daga jihar Kaduna a madadin sa, yana mai cewa shugaban kasan zai same shi da amfani sosai da kuma kwazo.

Mista Sani ya taba zama kwamishina a ma’aikatu uku a jihar Kaduna (ilimi da muhalli na kananan hukumomi) yayin da El-Rufai ke gwamna.

El-Rufai ya ziyarci shugaban ne a fadar shugaban kasa kwana guda bayan da majalisar dattawa ta tabbatar da sunayen ministoci 45 bayan shafe mako guda ana tantance 48 daga cikinsu.

Sai dai babban zauren majalisar ta ki amincewa da sahihancinsa da na wasu mutane biyu, saboda rahoton tsaro daga hukumar tsaro ta jihar kan matakin.

Sauran biyun dai sun hada da tsohon Sanata daga Taraba, Sani Danladi, da kuma ‘yar takarar jihar Delta, Stella Okotete.

Majiyarmu ta ce da sanin matakin da majalisar dattawan ta dauka kan karar sa, Mista El-Rufai, wanda kawai ya dawo Najeriya daga Landan ranar Litinin, ya nemi ya samu ganawa da shugaban.

A taron da aka yi a ranar Talata da yamma, Shugaba Tinubu, kamar yadda majiyar mu ta bayyana, ya shaida wa tsohon gwamnan cewa ya samu wasu korafe-korafe da ke sukar nadin nasa na minista.

Daga nan sai shugaban ya nemi a ba shi sa’o’i 24 domin ya duba koke-koke da kuma rahoton SSS ga majalisar dattawa domin samun damar yanke hukunci.

A wannan lokacin ne Mista El-Rufai ya mayar da martani da cewa ba ya sha’awar zama minista tunda ga dukkan alamu wasu dakaru da ke kusa da shugaban kasar na shirin hana shi zama ministan tarayya.

Mista El-Rufai ya bayyana a lokacin da yake sauraren kararrakin tabbatar da shi a ranar 1 ga watan Agusta cewa Mista Tinubu ya bukaci ya yi aiki tare da shi kan matsalar wutar lantarki da kasar nan ke fuskanta.

Firdausi Musa Dantsoho