JAMI’AN MULKIN SOJA A NIJAR SUN YI BARAZANAR KASHE BAZOUM IDAN AKA DAUKI MATAKIN SOJI A KANSU.

0
62

Rundunar sojan Nijar ta shaida wa wani babban jami’in diflomasiyyar Amurka cewa, za su kashe Bazoum idan kasashen da ke makwabtaka da kasar suka yi yunkurin shiga tsakani na soji don maido da mulkinsa, kamar yadda wasu jami’an kasashen yammacin duniya suka shaida wa kamfanin dillancin labaran AP.

Sun yi magana da kamfannin dillancin labarai na AP ne jim kadan kafin kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka ta ce ta ba da umarnin aikewa da “dakarun tsaro” don maido da mulkin dimokradiyya a Nijar, bayan wa’adin da ta diba na maido da Bazoum ya cika ranar Lahadi.

Shugabannin kasashe tara na kungiyar kasashen yammacin Afirka mai mambobi 15 sun gana jiya Alhamis a Abuja babban birnin Najeriya, domin tattauna matakin da za su dauka na gaba.Da yake magana bayan tattaunawar, shugaban hukumr ta ECOWAS, Omar Alieu Touray, ya ce zai iya sake tabbatar da shawarar da “hukumomin soji a yankin suka yanke na tura rundunar tsaro masu jiran umarnin cika aiki.”

Kungiyar ECOWAS dai ta kakabawa Nijar tsauraran takunkumin karya tattalin arziki da tafiye-tafiye, sai dai masu sharhi na ganin cewa za ta iya kubucewa hanyoyin da za a bi domin tallafa wa shiga tsakani.

Nnamdi Obasi, babban mai ba da shawara a kungiyar ta Crisis Group, ya ce ya kamata kungiyar ECOWAS ta kara yin nazari kan harkokin diflomasiyya a Nijar.

“Yin amfani da karfi zai iya haifar da sakamakon da ba a yi niyya ba da kuma bala’i tare da sakamako mara kyau,” in ji shi, yana mai gargadin cewa, shiga tsakani na soja zai iya haifar da “babban rikici na yanki” tsakanin gwamnatocin dimokradiyya da kuma kawancen gwamnatocin soja.Cameron Hudson, tsohon jami’in hukumar leken asiri ta Amurka CIA ya ce “Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU zai iya yin watsi da wannan shawarar ta ECOWAS idan har ta ga cewa ana yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a nahiyar.”

“Duk wani juyin mulkin da ya yi nasara sama da sa’o’i 24, ya zo zaman din-din-din ne. Don haka, lamarin shine cewa, suna nuna alamun ikon karfi ne,” in ji Oladeinde Ariyo, wani mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya. “Don haka, dole ne a yi shawara da su ta yadda su ke bukata.”

A halin da ake ciki,al’ummar Jamhuriyar Nijar, kimanin mutane miliyan 25 suna fama da tasirin takunkumin.

Wasu unguwanni a Yamai babban birnin kasar ba su da isasshen wutar lantarki kuma ana yawan samun katsewar wutar lantarki a cikin birnin. Kasar na samun kashi 90% na wutar lantarki daga Najeriya, wanda a halin yanzu, ta yanke wa wasu wutar lantarkin.

 

Daga Fatima Abubakar.