Sarakunan gargajiya goma ne daga babban birnin tarayya suka anfana da motocin alfarma.

0
12

Ministan babban birnin tarayya, Barista Ezenwo Nyesom Wike, ya mika motocin hukuma guda goma ga hakimai masu mataki na uku a babban birnin tarayya Abuja a wani yunkuri na tallafawa sarakunan gargajiya wajen yaki da rashin tsaro.

Wannan karimcin, in ji Ministan, ya yi daidai da sabon ajandar fatan da Shugaba Bola Tinubu ya yi, kuma yana da nufin karfafawa ubannin sarauta damar taka rawarsu yadda ya kamata.

A yayin gabatar da jawabin, Minista Wike ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin Hukumar FCT da sarakunan gargajiya wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin  babban birnin tarayya. Ya kuma bukaci sarakunan da su gudanar da ayyukansu da kyau, tare da yin koyi da irin yadda gwamnati ke yi a yankunansu.

Da yake mika godiya a madadin sarakunan gargajiya, Ona na Abaji kuma shugaban majalisar sarakunan babban birnin tarayya, Alhaji Adamu Baba Yunusa, ya godewa minista Wike da ya basu motocin. Ya kuma tabbatar wa da ministan da gwamnati cewa za su yi amfani da su wajen inganta zaman lafiya da tsaro a yankunansu.

Ana dai kallon gabatar da motocin na hukuma a matsayin wani mataki na karfafa alaka tsakanin gwamnati da sarakunan gargajiya,da suke aiki tare domin wanzar da zaman lafiya da tsaro a babban birnin tarayya Abuja.

Ana fatan da wannan tallafin, sarakunan za su samu nagartattun kayan aiki don magance matsalolin rashin tsaro a yankunansu da samar da karin zaman lafiya.

 

Daga Fatima Abubakar.