SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari da iyalansa sun koma gidan Glass House dake fadar shugaban kasa dake Abuja, gabanin bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ce ta bayyana hakan ta wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram bayan ta zagaya da uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu a gidan gwamnatin Tarayya.
A yayin ziyarar ta Villa, Aisha Buhari ta gabatar da Sanata Remi Tinubu a sassa daban-daban na gidan Gwamnatin, inda ta yi bayani dalla-dalla game da sake fasalin tarihi da mahimmancin kowane ginin.
A cewar Uwargidan Shugaban Kasar, Gidan Gilashin ya kasance gidan rikon kwarya ga shugaban kasa mai barin gado da kuma matansu a lokacin mika mulki.
Yana ba da sarari na alama kuma na zahiri ga shugaban mai barin gado,kuma yana ba da sarari ga shugaban mai jiran gado ya ɗauki cikakken iko.
Yayin da ta ke bayyana cewa ita da mijinta sun koma katafaren gidan,matan Buhari ta bukaci gwamnatocin da suka gaje su da su ci gaba da kasancewa shugaban kasa mai barin gado da matarsa su zauna a gidan gilashin har sai an kammala mika mulki.
“Na dauki uwargidan shugaban kasa mai jiran gado, Sanata Remi Tinubu domin ta ga lungu da sako na babban gidan. Ta ce a yanzu muna gidan gilas mai farin jini. Gidan gilashin gida ne na wucin gadi na shugaban mai barin gado.
“Ina ba da shawara cewa Gidan Gilashin ya ci gaba da al’adarsa ta zama sauyi ga shugaban kasa mai barin gado. Kamar yadda nake magana da ku yanzu, ina zaune a nan tare da mijina. Mu biyu ne kawai a nan, ina ganin ya kamata ya kasance a matsayin ka’idar cibiya da gidan,”
A nata jawabin bayan kammala rangadin, Sanata Tinubu ta yaba da damar da ta samu da kuma farin jinin uwargidan shugaban kasa mai masaukin baki.
“Na zagaya da kyar, ta nuna min a gidan,kuma cikin alheri ta bayyana mani abubuwa da yawa wanda a ɗan gajeren lokaci kuma yana da wuyar fahimta.
“Amma, na yi imani Allah zai taimake ni in iya ba da gudummawa mai tasiri ga al’umma,” in ji Sanata Tinubu.
Ta kara jaddada cewa ta yi imanin Allah Madaukakin Sarki zai taimake ta ta yi tasiri mai kyau da kuma gini kan abin da Aisha Buhari ta bari
Daga Fatima Abubakar.