Za a kaddamar da masallacin dindindin na yin sallar Juma’a da sauran salloli a majalisar dokokin Najeriya ranar 2 ga watan Yunin 2023 .

0
23

A karon farko tun bayan da aka fara taron majalisar dokokin tarayya Abuja, za a fara bude masallacin dindindin na yau da kullum da kuma sallar Juma’a a ranar Juma’a 26 ga watan Mayu.

Da yake kaddamar da kwamatin gudanarwa na mutum 7 a ofishinsa a yau, shugaban kwamitin gine-ginen masallacin Sanata Ibrahim Shekarau ya bukaci ‘yan kungiyar da su yi kokari wajen ganin an samu nasarar gudanar da aikin ba tare da bata lokaci ba.

Da yake mayar da martani a madadin ‘yan kwamitin, shugaban kuma dan majalisar wakilai Hon. Engr Yunusa Abubakar ya bada tabbacin jajircewar yan kungiyar tare da godewa Ubangiji da ya ba da ikon yin wannan aiki.

Ya yi kira ga ’yan uwa da su yi sadaukarwa saboda kankanin lokacin aikin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Honarabul Sanata Nasiru Sani Zagon Daura, Hon Isiyaka Ibrahim, Ustaz Sadiq Bala Illelah, Dr Sule Ya’u Sule yayin da Haruna Ibrahim Shekarau zai zama sakataren kwamitin.

 

Daga Fatima Abubakar.