Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyya Ga Iyalan Adamu Fika

0
30
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana alhininsa game da rasuwar Alhaji Adamu Fika. Alhaji Adamu fika wanda ya taba rike mukamin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya,  ya rasu A ranar Talata 25 ga watan shekarar 2023 ya rasu yana da shekaru 90 a duniya.
Ta’aziyyar shugaban na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mista Ajuri Ngelale ya fitar , a ranar Laraba a Abuja.
Cikin  ta’aziyyar da Shugaba Tinubu ya tura , ya tuno da irin rawar da Fika  ya taka a lokacin rayuwarsa  wajen raya cibiya mai dorewa da ke da alhakin zayyanawa da kuma aiwatar da manufofin jama’a ,a wani mawuyacin lokaci na ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Ya ce gudunmawar da Fika ya bayar a matsayinsa na shugaban ma’aikata da kuma shugaban kwamitin gyaran fuska na ma’aikata daban-daban, tarihinsa ba zai gushe ba,  a tarihin kasar  Najeriya .
“Alhaji Adamu Fika ya ci gaba da yi wa Najeriya hidima inda ya rike mukamai daban-daban, kafin a kai shi ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya; mukamin da ya rike har ya yi ritaya.”
Sannan ya  jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar  Yobe, Tinubu ya Kare da céwa marigayi  Fika mutum ne Wanda ya tsaya kan  abubuwan da suka haɗar da , gaskiya, kishin hidima, da jajircewar da ta dace a yi ma’aikatan gwamnati da sauran ‘yan uwa suyi ko Yi da su.
“Allah ya gafarta masa zunubansa, kuma ya ba shi Aljannar Firdausi,” in ji shugaban.
Hafsat Ibrahim