Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya Ya Karɓi Baƙuncin Matan Gwamnonin Yankin, Inda Ya Buƙaci A Ƙarfafa Ayyukan Ci Gaba Don Magance Ƙalubalen Dake Addabar Shiyyar
Hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwar da
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Ismaila Uba Misilli ya fitar tare da miƙa ta ga Mujalla da Gidan Talabijin na Tozali.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewan kuma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya yi ƙira da a ƙara ƙaimi ta fannin samar da ilimi da kiwon lafiya, da gina jama’a ta hanyar haɓaka kasuwanci da bunƙasa ƙwarewa don kyautata rayuwa da samar da wadata a yankin.
Gwamnan ya yi wannan ƙiran ne yayin da ya karɓi baƙuncin mambobin Ƙungiyar Matan Gwamnonin Arewa 19, NGWF a ziyarar ban girma da suka kai masa a gidan gwamnati dake Gombe.
Gwamnan yace yankin yana fama da ɗimbin ƙalubale waɗanda ke kawo cikas ga ci gabansa, yana mai jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar gwamnonin na Arewa da ƙungiyar matan nasu wajen shawo kan waɗannan ƙalubale.
Gwamna Inuwa ya nuna damuwa musamman kan yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewa da irin illar dake tattare da hakan ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
“Abin takaici ne cewa yankinmu ne ya fi kowanne yawan yaran da ba sa zuwa makaranta. Har yanzu kuma mutanenmu ba su rungumi sabin ƙudurorin ci gaban duniya ba”, in ji shi, yana mai jaddada muhimmiyar rawar da ilimi ke takawa wajen kawo sauyin da ake buƙata.
“Babu wani abu dake faruwa ba tare da ilimi ba; babu wani ci gaba da ke faruwa idan ba tare da shi ba. Ilimi yana kawo ci gaba, yana canza rayuwa, tare da inganta ta, har ma yana taimakawa wajen ciyar da jama’a gaba ta hanyar ci gaban zamani tare da ba mu damar fahimtar addininmu”, in ji shi.
Da yake tsokaci kan zaman lafiyar ƙasar nan, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin na Arewa ya yi nuni da cewa girman Arewacin Najeriya da yawan al’ummarta ya sa take da matuƙar muhimmanci ga zaman lafiyar ƙasar nan. Ya kuma yi gargadin cewa rashin tsaro da sauran matsalolin da ake fama da su a Arewa na iya kawo tabarbarewar zaman lafiyar ƙasar baki daya dama bazuwar hargitsi a yammacin Afirka.
Gwamna Inuwa ya kuma bayyana irin barazanar da ke tattare da shaye-shayen miyagun kwayoyi da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da ƙalubalen tsaro daban-daban da jihohi da dama ke fuskanta waɗanda suka haɗa da tashe-tashen hankula, da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane, da rikicin ƙabilanci.
Don haka ya buƙaci shugabanni a dukkan matakai da sauran masu ruwa da tsaki su tunkari waɗannan ƙalubale gadan-gadan.
Gwamnan na Gombe ya bayyana muhimmiyar rawar da matan gwamnonin za su iya takawa wajen inganta rayuwar al’umma musamman ta fuskar tallafawa mata da samar da shugabanci na gari, yana mai ba su tabbacin goyon bayansa a kan hakan.
“A matsayina na Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ina tabbatar muku da goyon bayana dana sauran gwamnonin, da kuma na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ƙarƙashin tsarinsa na sabunta fata wato ‘Renewed Hope Agenda’, “ƙarfafa haɗin gwiwa don inganta Najeriya.
Tun farko da take jawabi, Uwargidan Gwamnan Jihar Gomben, Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya kuma shugabar ƙungiyar matan gwamnonin Arewa, ta ce matan gwamnonin sun je Gombe ne don taronsu na bayan watanni uku -uku a ƙoƙarin da suke yi na ganin sun taimakawa mazajensu wajen bunƙasa tattalin arziƙi da zamantakewar Jihohinsu da ma yankin Arewa baki daya.
Dr Asma’u Inuwa Yahaya ta bayyana cewa taron nasu na Gombe ya maida hankali ne akan tallafawa mata da shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma barazanar yaran da basu zuwa makaranta, wanda ɗaya ne daga cikin manyan matsalolin dake kawo cikas ga ci gaban yankin.
Ta yaba da goyon bayan da suke samu daga Gwamnonin yankin na Arewa ƙarƙashin jagorancin Gwamnan na Gombe.