Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga mutum biyu tare da baje maboyar su.

0
45

Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce dakarun Operation Forest Sanity sun kashe wasu ‘yan bindiga biyu tare da fatattakar wasu maboya a karamar hukumar Chikun ta jihar.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida Mista Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kaduna ranar Talata.

Aruwan ya ce, “Bisa bayanin da rundunar ta samu ga gwamnatin jihar Kaduna, sojojin sun samu wadannan nasarori ne a lokacin da suke sintiri a dajin Kaboresha-Rijana-Kuzo-Kujeni da Gwanto-Kachia.

A cewarsa, sojojin sun yi kwanton bauna ne a kan hanyar Gwanto zuwa Kwasau, inda suka yi artabu da ‘yan bindiga da suka tunkari wurin.

“’Yan bindigar suna kan babura ne kuma an kashe biyu daga cikin masu laifin. Sun kwato babura uku,” inji shi.

“Sojojin sun kuma kai farmaki kan sansanonin ‘yan bindiga da ke yankin Kutura-Rijana bayan sun tsere zuwa cikin daji amma kuma an samu nasarar kwato babura uku.” Inji shi.

“Sauran abubuwan da aka kwato sun hada da kakin soja da dama da ‘yan bindiga,” in ji shi.

Aruwan ya ce za a ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan bindiga yayin da gwamnati ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu amfani ga jami’an tsaro.

Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna jin dadinsa kan nasarorin da aka samu yayin da ya yaba wa sojojin bisa jajircewarsu da nuna bajinta.

Daga Fatima Abubakar.