Sufeto janar na ‘yan sanda Usman Baba,ya amince da sabuwar kuma ingantattatun ka’idoji sanya tufafi ga mata jami’an da ke ba su damar sanya ‘yan Kunne da gyale a karkashin kakin su a lokacin aiki.
An bayyana tsarin suturar ne a taron IGP tare da manajojin ‘yan sanda dana dabaru a ranar 3 ga watan maris 2022.
Sufeto janar din ya nuna cewa,rundunar yan sandan Nijeriya tana da jami’ai daga kowace karamar hukuma a kasar da ke da bambance bambancen kabila da addini.
A wata sanarwar da jami’an hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar,ya ce hakan ya kawo bukatar tabbatar da hada kai,daidaita jinsi,bambancin kabilanci da addini a wuraren aiki domin samar da ingantaccen aiki da kwarewa.
Adejobi ya kara da cewa ,sauran kasashen da suka amince da irin wannan ka’idar sun hada da Canada,Amurka, Sweden, Turkey Turkiyya, Ostireliya,Ingila da sauran su.Sai dai ya ce tsarin ba na tilas ba ne.
Daga Fatima Abubakar.