A YAU NE AKA GURFANAR DA KYARI DA WASU MUTUM SHIDA A GABAN KOTU.

0
40

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta gurfanar da DCP Abba Kyari da wasu mutum shida a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babban kotun tarayya ta 8 da ke Abuja,bisa tuhumar aikata sarrafa miyagun kwayoyi.

A lokacin da aka karanta karar da ke cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CR/57/2022 ga wa’yanda ake tuhuma DCP Abba kyari, ACP J Ubia,ASP James Bawa,Sufeto Simon Agrigba,Sufeto John Nuhu,dukkanin jami’an da ake tuhuman sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da shi,yayin da Chibunna Patrick da Alfonsus Ezenwanne suka amsa laifin su.

Daga Fatima Abubakar.