TSOHON SARKIN KANO SANUSI LAMIDO YA GANA DA SHUGABAN JUYIN MULKIN SOJI A JAMHURIYAR NIJAR.

0
24

Tsohon Sarkin Kano, Lamido Sanusi ya gana da shugabannin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.

A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo yanzu haka, an ga Sanusi tare da Sarkin Damagaran a ziyarar da suka kai wa jagoran juyin mulkin Abdourahmane Tiani.

Damagaran shi ne birni na uku mafi girma a Nijar  Wannan dai na zuwa ne sa’o’i bayan shugabannin suka  soke wata ganawa da mukaddashin  sakatariyar Amurka, Victoria Nuland a ziyarar da ta kai Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.

Har ila yau gwamnatin mulkin sojan ta yi watsi da kiraye-kirayen da kungiyar Tarayyar Afirka ta yi mata, yayin da kuma ta ki amincewa da bukatar kungiyar kasashen yammacin Afirka kan maido da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum

 

    Daga Fatima Abubakar