Wani Fasinja ya yi aman Hodar Iblis 80, a filin saukar jirage saman Murtala Mohammed da ke Legas.

0
24

Wani Fasinja ya yi aman Hodar Iblis 80, a filin saukar jirage saman Murtala Mohammed da ke Legas.

Daga Shamsiyya Hamza Sulaiman

 

 

Rahotanni daga filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas sun ce, Jami’an hukumar Hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, sun cafke wani fasinja dan kasar Indiya, mai suna Freeman Charles Ogbonna a yayin tantance fasinjoji. Jami’an sun dai cafke fasinjar bisa zarginsa da shan hodar iblis.

Tozali Tv ta ruwaito cewa an kama Ogbonna ne a ranar Lahadi 31 ga watan Maris yayin da yake yunkurin hawa jirgin kasar Qatar, wato Qatar Airways zuwa birnin Delhi ta kasar Indiya, inda zai yada zango a birnin Doha kafin isarsa inda zai je.

An dai ce fasinjar na dauke ne da fasfo din kasar Laberiya mai suna: Carr Bismark.

A yayin da yake karin haske dangane lamarin, babban daraktan yada labarai na hukumar NDLEA, Femi Babafemi, a cikin wata takarda da ya sanya wa hannu ya ce:

Binciken farko da aka yi ya nuna ainihin sunan fasinjar Freeman Charles Ogbonna daga bisani kuwa, aka damka shi a hannun hukumar ta NDLEA inda ya fara nuna rashin gaskiyarsa a fili, wanda ya sanya har aka gano yana dauke da abun hana fitar da fitsari.

Ba da jimawa ba, in Femi, fasinjar ya fara yin amai tare da fitar da hodar iblis din da ya sha kusan lokaci guda.

Wanda ake zargn da ya yi ikirarin cewa daya daga cikin ‘yan’uwansa ne ya dauke shi aikin fataucin miyagun kwayoyi har ya hadiye jimillar hodar ibilis guda 80 mai nauyin gram 889 ta bakinsa da cusa wasu a duburarsa tsawon kwanaki hudu.ba tare da la’akari hadarin da zai haifa masa ba.

Ogbonna ya ce an ba shi magungunan ne don ya hadiye shi a wani otal da ke unguwar Ipodo a Ikeja, tare da yi masa alkawarin ba shi tsabar kudi N300,000 idan ya samu nasarar kai kayan a Indiya.

Hakazalika, a wani samamen kuwa, jami’an na NDLEA da ke filin jirgin saman Legas, a ranar Laraba 3 ga watan Afrilu, sun kama wani kasurgumin mutum mai suna Imran Taofeek Olalekan, a yayin kokarin hawa jirgin kasar Oman dauke da wasu jakunkuna.

Bincike mai zurfi a cikin jakar, ya sa aka gano wasu miyagun kwayoyin da aka cusa a can kasar jakar.

Hakan ta sanya Jami’an yin gaggawar damke mutumin, tare da wani wanda ya rako zuwa filin jirgin mai suna Ishola.

Wanda ake zargin Imran Taofeek Olalekan ya ce ya dawo daga Dubai shekarun da suka gabata amma har yanzu yana da takardar izinin zama a kasar. Ya yi ikirarin cewa an yi masa alkawarin Naira miliyan 1,500,000 idan ya samu nasarar kai kwayoyin zuwa kasar Oman, yayin da wanda ya dauka aiki, Ishola za a biya shi N200,000.

Binciken da Tozali TV ta yi, ta gano cewa an samu wata laya a jakunkunan da aka kama, inda suka tabatar da cewa wani malami ne a jihar oyo ya ba su domin neman sa’a da gujewa tarkon hukuma a yayin zirga zirga.

Har Ila yau Kuma, tashar jiragen ruwan Tincan da ke Legas, jami’an na NDLEA, a ranar Laraba 3 ga Afrilu, sun kama buhunnai 2,144 na haramtacciyar kwayar Colorado, da ganyen tabar wiwi mai nauyin kilo 1,072.

An dai ce jami’an sun yi nasarar kama shi ne a lokacin gwajin hadin gwiwa da Hukumar Kwastam da sauran masu ruwa da tsaki na wani akwati mai lamba GAOU 6699215 da ta fito daga Montreal, amma ta samo asali daga Toronto, Kanada.

An gano magungunan da ke kunshe a cikin jakunkuna 46 na jumbo da aka yi amfani da su a cikin motoci masu kirar 2009 Lexus RX 350, 2011 Toyota Sienna, da Lexus ES 350 na 2009 da kuma injinan da aka yi amfani da su, kofofin mota, tayoyi, da kayayyakin gida da aka yi amfani da su da kuma manyan ganguna da aka loda a cikin motocin.

 

 

Hafsat Ibrahim