Wani Plaza Mai Hawa Biyu Da Ke Unguwar Legas Street A Gundumar Garki Village Ya Rufta Da Mutane A Daren Jiya Laraba .

0
33

Wani Plaza mai suna Storey Plaza ya ruguje a daren Laraba a Abuja babban birnin Najeriya a kan titin Legas, unguwar Garki Village a gundumar Garki.

Da yake tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai a Abuja, Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Tarayya, Dakta Abbass Iddriss ya ce kawo yanzu an ceto mutane 37 a wurin da ginin ya ruguje.

Dokta Idriss ya ce an kwashe mutanen da abin ya shafa zuwa asibitoci daban-daban a Abuja.

Ya kuma tabbatar da cewa mutane biyu sun samu raunuka da ya yi muni

A cewar DG, ya zuwa yanzu an ceto mutane 37 tare da kwashe su zuwa Asibiti, wasu kuma rahotanni sun ce har yanzu suna makale.

“Tawagar ceto da sauran su suna nan a kasa.
Ana gudanar da aikin ceto amma sannu a hankali saboda ruwan sama da ake ci gaba da zubowa”.

Ya kara da cewa, “Suna yin namijin kokari wajen samun na’urar tona don kwashe mutane daga baraguzan ginin.”

Shugaban ya yaba da kokarin duk masu ruwa da tsaki da suke aiki tukuru da hannu wajen ceto mutanen da suka makale ciki har da al’umma.

Ya bayyana cewa ana ci gaba da aikin ceto yayin da suke jiran isowar kayan aiki don inganta ayyukan

 

Daga Fatima Abubakar.